Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 10:35 - Littafi Mai Tsarki

35 Yehu kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowahaz ɗansa ya gaji sarautarsa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

35 Yehu ya huta tare da kakanninsa, aka binne shi a Samariya. Yehoyahaz kuma ya ci sarauta bayansa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 10:35
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta ashirin da uku ta sarautar Yowash ɗan Ahaziya Sarkin Yahuza, Yehowahaz ɗan Yehu ya ci sarautar Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha bakwai.


Rehobowam kuwa ya rasu, aka binne shi a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Na'ama, ita kuwa Ba'ammoniya ce. Ɗansa, Abaija ya gāji sarautar.


Yerobowam ya yi mulki shekara ashirin da biyu sa'an nan ya rasu, aka binne shi. Ɗansa Nadab ya gāji sarautarsa.


Sa'an nan Dawuda ya rasu, aka binne shi a birnin Urushalima.


In ba haka ba, zai zama sa'ad da ka rasu za a ɗauka ni da ɗana, sulemanu, masu laifi ne.”


Sa'ad da kwanakinka suka ƙare, za ka rasu tare da kakanninka. A bayanka, zan ta da ɗanka, na cikinka. Zan sa mulkinsa ya kahu.


Sauran ayyukan Yehu da dukan abin da ya yi, da dukan ƙarfinsa an rubuta su a littafin tarihin sarakuna Isra'ila.


Yehu ya yi mulkin Isra'ila a Samariya shekara ashirin da takwas.


Ubangiji kuwa ya ce wa Yehu, “Da yake ka yi abin da yake daidai a gare ni, ka yi wa gidan ahab bisa ga dukan abin da yake a zuciyata, 'ya'yanka, har tsara ta huɗu, za su ci sarautar Isra'ila.”


Yehowahaz kuwa ya rasu, aka binne shi a Samariya. Yehowash ɗansa ya gāji sarautarsa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ