Suka kuwa yi shelar azumi, suka sa Nabot a gaban jama'a. 'Yan iska guda biyu suka zauna kusa da shi, suka yi ta zarginsa a gaban jama'a, suna cewa, “Nabot ya zagi Allah da sarki.”
Ya karɓi zobban a hannunsu, sai ya narkar da su, ya sassaƙa shi da kurfi, ya siffata ɗan maraƙi. Da jama'a suka gani, sai suka ce, “Allahnku ke nan, ya Isra'ila, wanda ya fisshe ku daga Masar.”