2 Sarakuna 10:15 - Littafi Mai Tsarki15 Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?” Yehonadab ya amsa, “I.” Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202015 Bayan ya bar wurin, sai ya gamu da Yehonadab ɗan Rekab wanda yake kan hanyarsa don yă sadu da shi. Sai Yehu ya gaishe shi, ya ce, “Ka amince da ni yadda na amince da kai?” Yehonadab ya ce, “I.” Yehu ya ce, “To, in haka ne ka ba ni hannunka.” Sai ya miƙa masa, Yehu kuwa ya ja shi cikin keken yaƙin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |