2 Sarakuna 10:14 - Littafi Mai Tsarki14 Yehu kuwa ya ce, “Ku kama su da rai.” Sai suka kama su da rai, suka karkashe su a ramin Bet-eked, su arba'in da biyu ne, ba a rage ko ɗaya a cikinsu ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202014 Sai ya umarta ya ce, “A kama su da rai!” Aka kuwa kama su aka yayyanka kusa da rijiyar Bet-Eked, su arba’in da biyu. Ba a bar wani da rai ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'an nan Yehu ya rubuta musu wasiƙa ta biyu, ya ce, “Idan kuna goyon bayana, idan kuma kun shirya za ku yi mini biyayya, to, sai ku fille kawunan 'ya'yan Ahab, sa'an nan ku zo wurina a Yezreyel gobe war haka.” 'Ya'yan sarki, maza, su saba'in ne, suna a hannun manyan mutanen birni ne waɗanda suke lura da su.
Da ya tashi daga can, sai ya sadu da Yehonadab ɗan Rekab yana zuwa ya tarye shi. Yehu ya gaishe shi, ya tambaye shi, “Zuciyarka ta amince da ni kamar yadda tawa ta amince da kai?” Yehonadab ya amsa, “I.” Sai Yehu ya ce, “Idan haka ne, to, miƙo mini hannunka.” Sai ya miƙa masa hannunsa. Yehu kuwa ya ɗauke shi zuwa cikin karusa.