Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 1:8 - Littafi Mai Tsarki

8 Suka ce masa, “Ai, wani gargasa ne mai ɗamara ta fata.” Sarki ya ce, “Ai, Iliya ne Batishbe.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

8 Sai suka ce, “Mutumin ya sa riga mai gashi, ya kuma yi ɗamara da fata.” Sarkin ya ce, “Ai, Iliya mutumin Tishbe nan ne.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 1:8
9 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yahaya kuwa yana saye da tufa ta gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.


A wannan rana ce kowane annabi zai ji kunyar wahayinsa sa'ad da ya yi annabcin. Ba zai sa rigar gashi don ya ruɗi jama'a ba.


Yahaya kuwa na sanye da tufar gashin raƙumi, yana kuma ɗaure da ɗamara ta fata, abincinsa kuwa fara ce da ruwan zuma.


Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”


Zai riga shi gaba cikin ruhu da iko irin na Iliya. Yă mai da hankalin iyaye a kan 'ya'yansu, Yă kuma juyo da marasa biyayya su bi hikimar adalai, Ya tanada wa Ubangiji jama'a, ya same su a shirye.”


To, kallon me kuka fita? Wani mai adon alharini? Ai kuwa, masu adon alharini a fada suke.


A wannan lokaci Ubangiji ya riga ya faɗa wa Ishaya ɗan Amoz, cewa ya tuɓe tsummokin da yake saye da su, ya kuma tuɓe takalmansa. Shi kuwa ya yi biyayya ya yi ta yawo tsirara, ba kuma takalmi a ƙafarsa.


Sarki ya tambaye su, “Yaya mutumin yake, shi wanda ya sadu da ku, ya faɗa muku irin wannan magana?”


Ubangiji kuwa ya saukar wa Iliya da iko, ya sha ɗamara, ya sheka a guje, ya riga Ahab isa Yezreyel.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ