Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Sarakuna 1:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Ahaziya kuwa ya mutu bisa ga maganar Ubangiji, daidai yadda Iliya ya faɗa. Sai ɗan'uwansa Yehoram ya gāji gadon sarautarsa a shekara ta biyu ta Yoram ɗan Yehoshafat Sarkin Yahuza, gama Ahaziya ba shi da ɗa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ya kuwa mutu yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya. Da yake Ahaziya ba shi da ɗa, sai Yoram ya gāje shi, ya zama sarki a shekara ta biyu ta mulkin Yehoram, ɗan Yehoshafat, sarkin Yahuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Sarakuna 1:17
11 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A shekara ta goma sha takwas ta sarautar Yehoshafat Sarkin Yahuza, Yehoram ɗan Ahab ya zama Sarkin Isra'ila a Samariya. Ya yi mulki shekara goma sha biyu.


Ahaziya, ɗan Ahab, ya ci sarautar Isra'ila a Samariya a shekara ta goma sha bakwai ta sarautar Yehoshafat, Sarkin Yahuza. Ya yi sarautar Isra'ila shekara biyu.


Sauran ayyukan da Ahaziya ya yi, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.


Nan fa, a ƙasar Mowab, Musa bawan Ubangiji, ya rasu kamar yadda Ubangiji ya faɗa.


Garin da yake cikin tukunyar bai ƙare ba, kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin Iliya.


Suka wanke karusarsa a tafkin Samariya. Karnuka suka lashe jininsa, karuwai kuma suka yi wanka a tafkin kamar yadda Ubangiji ya faɗa.


Yehoshafat yana da shekara talatin da biyar sa'ad da ya ci sarauta. Ya yi shekara ashirin da biyar yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Azuba 'yar Shilhi.


Sai suka komo, suka faɗa masa. Sai ya ce musu, “Wannan, ai, faɗar Ubangiji, wadda ya faɗa ta bakin bawansa Iliya Batishbe, ya ce, ‘Karnuka za su cinye naman Yezebel a cikin Yezreyel.


Da suka isa Samariya, sai ya kashe duk wanda ya ragu na gidan Ahab a Samariya. Ya share mutanen gidan Ahab kaf kamar yadda Ubangiji ya faɗa ta bakin annabi Iliya.


Yehoshafat ɗansa kuwa ya gāji gadon sarautarsa, ya kahu sosai gāba da Isra'ila.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ