Sa'an nan ya ci Mowabawa da yaƙi. Ya sa su su kwanta a ƙasa sa'an nan ya riƙa auna su da igiya, kowane awo biyu ya sa a kashe su, awo na uku kuwa sai ya sa a bar su da rai. Mowabawa suka zama talakawansa, suka riƙa kawo haraji.
Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.