Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 8:6 - Littafi Mai Tsarki

6 Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

6 Ya ajiye ƙungiyoyi sojoji a masarautar Arameyawan Damaskus, Arameyawa kuwa suka zama bayinsa, suka biya shi haraji. Ubangiji ya ba Dawuda nasara a duk inda ya tafi.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 8:6
26 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a ƙasar Edom duka. Edomawa suka zama talakawan Dawuda. Ubangiji ya ba Dawuda nasara duk inda ya tafi.


Ya Ubangiji, Allahna, Mai Cetona, mai ƙarfi, Kā kiyaye ni cikin yaƙi.


Ya sa sojoji a kowane birni mai kagara a Yahuza, ya kuma sa ƙungiyoyin sojoji masu tsaro a ƙasar Yahuza, da kuma a biranen Ifraimu waɗanda tsohonsa Asa ya ci da yaƙi.


Ban kuwa rabu da kai ba duk inda ka tafi, na kuma kawar da abokan gābanka duka. Zan sa ka shahara kamar shahararrun mutane na duniya.


Kana iya shirya dawakai don zuwa yaƙi, amma nasara ta Ubangiji ce.


Sai ya sa ƙungiyoyin sojoji a Edom, dukan Edomawa kuma suka zama bayin Dawuda. Ubangiji kuwa ya taimaki Dawuda duk inda ya tafi.


Dawuda yana cikin kagara, ƙungiyar sojojin Filistiyawa kuwa tana a Baitalami.


Sa'an nan ya ci Mowabawa da yaƙi. Ya sa su su kwanta a ƙasa sa'an nan ya riƙa auna su da igiya, kowane awo biyu ya sa a kashe su, awo na uku kuwa sai ya sa a bar su da rai. Mowabawa suka zama talakawansa, suka riƙa kawo haraji.


To, yanzu sai ku yarda ya sarauce ku, gama Ubangiji ya yi wa Dawuda alkawari ya ce, ‘Ta hannun bawana, Dawuda, zan ceci jama'ar Isra'ila daga hannun Filistiyawa, da na dukan abokan gābansu.’ ”


Dukan Filistiyawan da suke a filin suka ji tsoro, da mahara da sauran sojoji suka yi rawar jiki, ƙasa ta girgiza, aka yi babbar gigicewa.


Jonatan ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye zuwa sansanin marasa kaciyan nan, arnan nan, watakila Ubangiji zai yi aiki ta wurinmu, gama ba abin da zai hana Ubangiji ya yiwo ceto ta wurin masu yawa, ko kuwa ta wurin 'yan kaɗan.”


Wata rana Jonatan, ɗan Saul, ya ce wa saurayin da yake ɗaukar masa makamai, “Zo, mu haye mu je sansanin Filistiyawa a wancan hayi.” Amma bai faɗa wa mahaifinsa ba.


Jonatan kuwa ya kashe wani shugaban yaƙi na Filistiyawa a Geba, Filistiyawa kuwa suka ji labarin abin da ya faru. Sai Saul ya sa aka busa ƙaho ko'ina a ƙasar, na kiran Ibraniyawa su zo yaƙi.


Dawuda ya kwashe garkuwoyi na zinariya waɗanda shugabannin sojojin Hadadezer suka riƙe, ya kawo su Urushalima.


Sa'ad da dukan hakiman Hadadezer suka ga Isra'ilawa sun ci su, sai suka yi sulhu da Isra'ilawa. Suka zama talakawansu. Wannan ya sa Suriyawa suka ji tsoron ƙara kai wa Ammonawa gudunmawa.


Sulemanu ya sarauci dukan mulkoki tun daga Kogin Yufiretis a gabas, har zuwa ƙasar Filistiyawa a yamma, daga kudu kuma har zuwa iyakar Masar. Su kuwa suka yi ta kawo wa Sulemanu harajinsu, ya kuwa mallake su dukan kwanakin ransa.


Dawuda kuwa ya ƙasaita, gama Ubangiji Allah Mai Runduna yana tare da shi.


Bayan rasuwar Ahab, Sarkin Isra'ila, sai Mowabawa suka tayar wa Isra'ilawa.


Mesha Sarkin Mowab kuwa makiyayin tumaki ni. Yakan ba Sarkin Isra'ila 'yan tumaki dubu ɗari (100,000), da raguna dubu ɗari (100,000) duk da ulunsu, gandu a shekara.


Sauran ayyukan Yerobowam na biyu, da dukan abin da ya yi, da ƙarfinsa, da yaƙi da ya yi, da yadda ya ƙwato wa Isra'ila Dimashƙu da Hamat waɗanda suke na Yahuza, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.


Ubangiji kuwa ya kasance tare da shi, duk inda ya nufa sai ya sami albarka. Ya tayar wa Sarkin Assuriya, ya ƙi bautar masa.


Da gaske ka yashe mu ke nan? Ba za ka yi tafiya tare da sojojinmu ba?


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ