Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 8:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Dawuda ya ƙwace masa mahayan dawakai dubu ɗaya da ɗari bakwai (1,700), da sojojin ƙafa dubu ashirin (20,000). Dawuda ya yanyanke agarar dawakan, sai dai doki ɗari ne ya bari.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Dawuda ya kame keken yaƙinsa guda dubu, mahayan keken yaƙinsa dubu bakwai, da sojojin ƙasa dubu ashirin. Ya yayyanke agaran dawakan duka amma ya bar dawakai kekunan yaƙi ɗari.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 8:4
8 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Joshuwa kuwa ya yi musu kamar yadda Ubangiji ya umarce shi, ya daddatse agaran dawakansu, ya kuma ƙone karusansu.


Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Joshuwa, “Kada ka ji tsoronsu, gama gobe war haka zan ba da su ga Isra'ilawa, su karkashe su duka. Za ku daddatse agaran dawakansu, ku kuma ƙone karusansu.”


Waɗansu ga karusan yaƙinsu suke dogara, Waɗansu kuwa ga dawakansu, Amma mu, ga ikon Ubangiji Allahnmu muke dogara!


Sai Dawuda ya ƙwace karusai dubu (1,000), da mahayan dawakai dubu bakwai (7,000), da sojojin ƙasa dubu ashirin (20,000) daga gare shi. Dawuda kuma ya yanyanke agarar dawakan da suke jan karusai, amma ya bar waɗansu dawakai daga cikinsu waɗanda suka isa jan karusai ɗari.


Sulemanu kuwa ya tattara karusai da mahayan dawakai. Yana da karusai dubu da ɗari huɗu (1,400), da mahayan dawakai dubu goma sha biyu (12,000), waɗanda ya zaunar da su a biranen karusai da kuma waɗansu tare da shi a Urushalima.


Amma kada sarkin ya tattara wa kansa dawakai, kada kuma ya sa mutane su tafi Masar don su ƙaro masa dawakai, tun da yake Ubangiji ya riga ya yi muku kashedi da cewar, ‘Kada ku sāke komawa can.’


Ba zan shiga shawararsu ta asiri ba, Ba kuwa zan sa hannu cikin taronsu ba, Gama cikin fushinsu suka kashe mutane, Cikin gangancinsu kuma suka gurgunta bijimai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ