Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 8:12 - Littafi Mai Tsarki

12 wato azurfa da zinariya na Edomawa, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, Sarkin Zoba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 wato, azurfa da zinariyan mutanen Edom, da na Mowabawa, da na Ammonawa, da na Filistiyawa, da na Amalekawa, da ganimar Hadadezer ɗan Rehob, sarkin Zoba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 8:12
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai suka shiga birnin. Sa'an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙi da Ammonawa.


Sarki Dawuda kuwa ya keɓe waɗannan ga Ubangiji, tare da azurfa da zinariya waɗanda ya kwaso daga al'umman da ya ci, wato Edom, da Mowab, da mutanen Ammon, da na Filistiya, da na Amalek.


Sa'an nan ya ci Mowabawa da yaƙi. Ya sa su su kwanta a ƙasa sa'an nan ya riƙa auna su da igiya, kowane awo biyu ya sa a kashe su, awo na uku kuwa sai ya sa a bar su da rai. Mowabawa suka zama talakawansa, suka riƙa kawo haraji.


Ya ce musu, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, ku kawo mini gudunmawa, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinku, sai in kai muku gudunmawa.


Ya kuma ƙwato garkunan tumaki, da na awaki, da na shanu. Mutanensa suka koro shanun, suka yi gaba, suka ce, “Wannan shi ne ganimar Dawuda.”


Dawuda yakan fita da mutanensa su kai wa Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa hari. Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.


ya kama Agag Sarkin Amalekawa da rai, ya hallaka mutane ƙaƙaf da takobi.


Sai Dawuda ya yi ta karkashe su tun faɗuwar rana har zuwa kashegari da yamma. Ba wanda ya tsira daga cikinsu sai samari ɗari huɗu waɗanda suka tsere a kan raƙuma.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ