2 Samaʼila 7:8 - Littafi Mai Tsarki8 Abin da za ka faɗa wa bawana Dawuda ke nan, in ji Ubangiji Mai Runduna, ‘Na ɗauko ka daga makiyaya inda kake kiwon tumaki domin ka zama sarkin jama'ata Isra'ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20208 “Yanzu, ka gaya wa bawana Dawuda ‘Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki ya ce, na ɗauko ka daga makiyaya, daga kuma garken tumaki ka zama sarki bisan mutane Isra’ila. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Dawuda ya ce wa Allah, “Ai, ni ne na ba da umarni a ƙidaya jama'ar. Hakika, ni na yi zunubi, na kuwa aikata mummunan abu, amma waɗannan talakawa fa, me suka yi? Ya Ubangiji Allahna, ka bar hannunka ya yi gāba da ni da gidan tsohona, amma kada ka yi gāba da jama'arka, har da za ka aukar musu da annoba.”