Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.
‘Tun daga ran da na fito da mutanena Isra'ila, daga Masar, ban zaɓi wani birni daga cikin kabilan Isra'ila inda zan gina Haikali domin sunana ba, amma na zaɓi Dawuda ya shugabanci mutanena Isra'ilawa.’ ”