Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 7:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Natan kuwa ya ce wa sarki, “Sai ka yi abin da yake a zuciyarka, gama Ubangiji yana tare da kai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Natan ya amsa wa sarki ya ce, “Duk abin da yake a zuciyarka, sai ka yi, gama Ubangiji yana tare da kai.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 7:3
14 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dawuda kuwa ya ce wa Sulemanu, “Ɗana, na ƙudura a zuciyata in gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allah.


Sarki Dawuda fa ya miƙe tsaye, ya ce, “Ku saurare ni, ku 'yan'uwana, da jama'ata. Na yi niyya a zuciyata in gina wa akwatin alkawari na Ubangiji wurin hutawa, da wurin zaman zatin Allah. Na riga na yi shiri domin ginin,


Sa'ad da ta isa wurin annabi Elisha a kan dutsen, sai ta kama ƙafafunsa. Sai Gehazi ya zo zai ture ta. Amma mutumin Allah ya ce masa, “Ƙyale ta kurum, gama tana da baƙin ciki ƙwarai, Ubangiji kuwa ya ɓoye mini abin.”


Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka kula da kyan tsarinsa, ko tsayinsa, domin ba shi nake so ba, gama yadda Ubangiji yake gani, ba haka mutum yake gani ba. Mutum yakan dubi kyan tsari ne kawai, amma Ubangiji yakan dubi zuciya.”


Ku kam, shafar nan da kuka samu daga Ruhu Mai Tsarki tā tabbata a zuciyarku, ba sai wani ya koya muku ba. Amma kamar yadda shafar nan tasa take koya muku kome, ita kuwa gaskiya ce ba ƙarya ba, yadda dai ta koya muku, to, sai ku zauna a cikinsa.


Ka nemi farin cikinka a wurin Ubangiji, Zai kuwa biya maka bukatarka.


Ya ba ka abin da kake bukata, Ya sa dukan shirye-shiryenka su yi nasara.


Sa'ad da waɗannan alamu suka cika, sai ka yi abin da hali ya nuna maka, gama Ubangiji yana tare da kai.


Amma a daren nan Ubangiji ya yi magana da Natan.


Sai mai ɗaukar masa makamai ya ce, “Ka yi abin da yake a zuciyarka, ga shi, ina tare da kai, gama ina goyon bayanka, kamar yadda zuciyarka take haka kuma tawa.”


Amma Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da annabi Natan, da Shimai, da Reyi, da masu tsaron lafiyar Dawuda, ba su goyi bayan Adonija ba.


An fa rubuta ayyukan sarki Dawuda daga farko har ƙarshe a tarihin Sama'ila, annabi, da na annabi Natan, da na annabi Gad.


Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ