Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 7:2 - Littafi Mai Tsarki

2 sai sarki ya ce wa annabi Natan, “Duba, ga shi, ina zaune a gidan katakon al'ul, amma akwatin alkawarin Ubangiji yana a alfarwa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 sai ya ce wa annabi Natan, “Ga ni, ina zama a fadar katakon al’ul, amma akwatin alkawarin Allah yana zaune a tenti.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 7:2
24 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Hiram Sarkin Taya ya aiki jakadu zuwa wurin Dawuda. Ya kuma aika masa da katakan itacen al'ul, da kafintoci, da masu yin gini da duwatsu, suka kuwa gina wa Dawuda gida.


Sai Ubangiji ya aiki Natan wurin Dawuda. Ya je wurinsa ya ce masa, “Akwai waɗansu mutum biyu a cikin wani gari. Ɗayan basarake ne, attajiri, ɗayan kuwa talaka ne, matalauci.


wanda ya sami tagomashi wurin Allah, har ya nemi alfarmar yi wa Allahn Yakubu masujada.


Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.”


“Ashe, lokaci ya yi da za ku zauna a ɗakunan da kuka yi wa rufin katako, amma Haikalin nan yana zaman kufai?


An fa rubuta ayyukan sarki Dawuda daga farko har ƙarshe a tarihin Sama'ila, annabi, da na annabi Natan, da na annabi Gad.


Suka fa shigo da akwatin alkawarin Allah, suka ajiye shi a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa masa, suka miƙa hadayu na ƙonawa da na salama a gaban Allah.


Sai sa'ad da na shirya wa Ubangiji wuri, Wato Haikali domin Maɗaukaki, Allah na Isra'ila.”


Amma dai Dawuda ya riga ya ɗauko akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim, ya kawo shi a wurin da ya shirya, gama ya kafa masa alfarwa a Urushalima.


Sai Hiram Sarkin Taya ya aiki manzanni wurin Dawuda, su kai masa itatuwan al'ul, da magina, da massassaƙa domin a gina masa fāda.


Haka kuwa Natan ya faɗa wa Dawuda dukan abin da Allah ya bayyana masa.


Suka kawo akwatin alkawarin Ubangiji, suka ajiye shi a wurinsa a cikin alfarwar da Dawuda ya kafa dominsa. Dawuda ya miƙa hadayun ƙonawa da na salama a gaban Ubangiji.


Ya kawo akwatin a cikin alfarwa, sa'an nan ya sa labulen don kāre akwatin alkawari, kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.


Uriya ya ce wa Dawuda, “Akwatin alkawari, da mutanen Isra'ila, da na Yahuza, suna zaune a bukkoki. Shuganana Yowab, da barorinsa suna zaune a sansani a karkara, ƙaƙa ni zan tafi gidana in ci in sha, in kwanta da matata? Na rantse da ranka, ba zan yi haka ba.”


Tana cikin magana da sarki, sai annabi Natan ya zo.


Sulemanu ya ci gaba, ya ce, “Tsohona, Dawuda ya yi niyyar gina wa Ubangiji Allah na Isra'ila ɗaki,


Dawuda kuwa ya ce wa Sulemanu, “Ɗana, na ƙudura a zuciyata in gina Haikali saboda sunan Ubangiji Allah.


Sauran ayyukan Sulemanu daga farko har ƙarshe an rubuta su a tarihin annabi Natan. An kuma rubuta su a annabcin Ahaija Bashilone, da kuma a wahayin Iddo maigani, game da Yerobowam ɗan Nebat.


Sai ya zaunar da Lawiyawa a Haikalin Ubangiji, masu kuge, da molaye, da garayu, bisa ga umarnin Dawuda, da na Gad, maigani na sarki, da na annabi Natan. Gama umarnin daga wurin Ubangiji ya zo ta wurin annabawansa.


Amma Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da annabi Natan, da Shimai, da Reyi, da masu tsaron lafiyar Dawuda, ba su goyi bayan Adonija ba.


Ka tuna, ya Ubangiji, da alkawarin da ya yi, Da rantsuwar da ya yi maka, ya Maɗaukaki, Allah na Isra'ila,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ