2 Samaʼila 7:10 - Littafi Mai Tsarki10-11 Zan nuna wa jama'ata Isra'ila wuri na kansu inda zan kafa su su zauna. Ba wanda zai sāke damunsu. Mugayen mutane kuma ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, tun lokacin da na naɗa wa jama'ata Isra'ila mahukunta. Zan hutar da kai daga fitinar abokan gābanka duka. Banda wannan kuma ina shaida maka, cewa, zan sa gidanka ya kahu. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Zan kuma tanada wa mutanena Isra’ila wuri, in kuma dasa su yadda za su kasance da gida kansu ba tare da an ƙara damunsu ba. Mugayen mutane ba za su ƙara wahalshe su kamar dā ba, အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Isra'ila ita ce gonar inabin Ubangiji Mai Runduna, Jama'ar Yahuza su ne itatuwan inabin da aka daddasa. Ya sa zuciya za su yi abin da yake mai kyau, Amma a maimakon haka sai suka zama masu kisankai! Ya zaci za su aikata abin da yake daidai, Amma waɗanda suka fāɗa hannunsu kururuwa suke, suna neman adalci!