2 Samaʼila 6:7 - Littafi Mai Tsarki7 Ubangiji ya husata da Uzza, ya buge shi, ya mutu nan take kusa da akwatin alkawarin Allah, saboda ya taɓa akwatin alkawari. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 20207 Fushin Ubangiji kuwa ya ƙuna a kan Uzza domin aikin rashin bangirma, saboda haka Allah ya buge shi ya kuma mutu a can kusa da akwatin alkawarin Allah. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sa'ad da Haruna da 'ya'yansa maza suka gama kintsa Wuri Mai Tsarki da kayayyakinsa duka a lokacin tashi, sai 'ya'yan Kohat, maza, su zo su ɗauke kayayyakin, amma kada su taɓa abubuwan nan masu tsarki domin kada su mutu. Waɗannan su ne ayyukan 'ya'yan Kohat a duk lokacin da za a naɗe alfarwa ta sujada.