Sa'ad da wannan lokaci ya yi, mata bakwai za su riƙe mutum guda su ce, “Mā iya ciyar da kanmu, mu kuma tufasar da kanmu, amma in ka yarda, bari mu ce kai ne mijinmu, domin kada mu sha kunyar zaman gwagwarci.”
Daga ran nan Sama'ila bai ƙara saduwa da sarki Saul ba, har rasuwar Sama'ila, amma ya ji juyayin Saul. Ubangiji kuwa bai ji daɗi da ya sa Saul ya zama Sarkin Isra'ila ba.