Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 6:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Da Dawuda ya komo gida domin ya sa wa iyalinsa albarka, Mikal, 'yar Saul, ta fito domin ta tarye shi, ta ce masa, “Ƙaƙa Sarkin Isra'ila ya ɗauki kansa yau? Ya kware darajarsa a gaban barorinsa mata kamar yadda shakiyyai suke yi.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Da Dawuda ya koma gida don yă sa wa gidansa albarka, sai Mikal ’yar Shawulu ta fito don tă tarye shi, sai ta ce, “Tabbas sarkin Isra’ila ya fiffita kansa yau, ya tuɓe a gaban bayinsa ’yan mata, kamar yadda duk marar kunya yakan yi!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 6:20
23 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal, 'yar Saul, ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta raina shi a zuci.


Dawuda ya sa falmaran ta lilin. Ya kuwa yi rawa da dukan ƙarfinsa a gaban Ubangiji.


Suka kuma ba shi azurfa saba'in daga cikin gidan gunkin nan Ba'al-berit. Da wannan azurfa Abimelek ya yi ijarar 'yan iska waɗanda suka bi shi.


Da 'yan'uwansa suka ji haka, sai suka fita su kamo shi, saboda sun ce, “Ai, ya ruɗe.”


Abin da nake yi ba zai zama laifi ba, Yaushe za ka zo wurina? Da zuciya mai tsabta zan zauna a gidana.


Ina yabonka, ya Ubangiji saboda ka cece ni, Ka kuwa hana magabtana su haɗiye ni.


Mutane ne marasa hankali marasa suna! Aka kore su daga ƙasar.


Sa'an nan dukan jama'a suka watse, kowa ya koma gidansa, Dawuda kuma ya koma gidansa, ya sa wa iyalinsa albarka.


Sa'ad da ya gama miƙa hadayun ƙonawa da na salama, sai ya sa wa mutanen albarka da sunan Ubangiji Mai Runduna.


Idan ba ku da nufi ku bauta wa Ubangiji, to, yau sai ku zaɓi wanda za ku bauta wa, ko gumakan da kakanninku suka bauta wa a wajajen hayin Kogin Yufiretis, ko kuma gumakan Amoriyawa waɗanda kuke zaune a ƙasarsu, amma ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.”


Gama na zaɓe shi don ya umarci 'ya'yansa da gidansa domin su kiyaye tafarkin Ubangiji a bayansa, su riƙe adalci da shari'a.” Ubangiji ya tabbatar wa Ibrahim da abin da ya alkawarta masa.


Sai ya zo kan Bitrus, shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ashe, kai ne za ka wanke mini ƙafa?”


Bitrus kuwa na ƙasa a filin gida, sai wata baranyar babban firist ta zo.


'Ya'yan Saul, maza ke nan, Jonatan, da Yishwi, da Malkishuwa. Yana kuma da 'ya'ya mata biyu, Merab, 'yar fari, da Mikal.


Ya kuma rarraba wa dukan taron jama'ar Isra'ila, mata da maza, ƙosai, da nama, da zabibi, sa'an nan dukan mutane suka watse, kowa ya tafi gidansa.


Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, gama don me za ka mutu tun kwanakinka ba su cika ba?


Mikal, 'yar Saul kuwa, ta ƙaunaci Dawuda, sai aka faɗa wa Saul, shi kuwa ya yarda da haka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ