Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 6:12 - Littafi Mai Tsarki

12 Aka faɗa wa Dawuda sarki, cewa, Ubangiji ya sa wa gidan Obed-edom albarka, da dukan abin da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Sai Dawuda ya tafi da murna ya kawo akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-edom zuwa Birnin Dawuda.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

12 To, sai aka faɗa wa Sarki Dawuda cewa, “Ubangiji ya sa wa gidan Obed-Edom albarka da dukan abin da yake da shi, saboda akwatin alkawarin Allah.” Saboda haka sai Dawuda ya gangara ya hauro da akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-Edom zuwa Birnin Dawuda da farin ciki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 6:12
16 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Haka Dawuda, da dattawan Isra'ilawa, da shugabannin dubu dubu, suka tafi da murna domin su ɗauko akwatin alkawarin Ubangiji daga gidan Obed-edom.


Kowa ya ba ɗaya daga cikin 'yan yaran nan, ko da moɗa guda ta baƙin ruwa, kan shi almajirina ne, hakika, ina gaya muku, ba zai rasa ladarsa ba.”


Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.


Duk da haka Dawuda ya ci kagarar Sihiyona, wato birnin Dawuda.


Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama'ar Isra'ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona.


Dukan dattawan Isra'ila suka zo, sai firistoci suka ɗauki akwatin alkawarin,


suka kawo tare da alfarwa ta sujada, da dukan tsarkakan tasoshin da suke cikin alfarwar. Firistoci da Lawiyawa suka kawo su.


Lawiyawa fa suka ɗauki akwatin alkawarin Allah a bisa sandunansa a kafaɗunsu, kamar yadda Musa ya umarta bisa ga maganar Ubangiji.


Yarjejeniyar da ya yi da Ibrahim, Da alkawarin da ya yi wa Ishaku.


Obed-edom kuma Allah ya ba shi 'ya'ya maza, su ne Shemaiya, da Yehozabad, da Yowa, da Sakar, da Netanel,


da Ammiyel, da Issaka, da Fauletai, da su Allah ya sa masa albarka.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ