Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.
A ni kaina ba zan ɗauki kome ba illa abin da samari suka ci, da rabon mutanen da suka tafi tare da ni. Sai dai kuma Aner, da Eshkol, da Mamre su ɗauki nasu rabo.”
Haka fa, Dawuda ya tattara dukan Isra'ilawa wuri ɗaya, daga Shihor ta Masar, har zuwa mashigin Hamat domin a kawo akwatin alkawari na Allah daga Kiriyat-yeyarim.