Sa'ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal, 'yar Saul, ta leƙa ta taga, ta ga sarki Dawuda yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta raina shi a zuci.
Aka faɗa wa Dawuda sarki, cewa, Ubangiji ya sa wa gidan Obed-edom albarka, da dukan abin da yake da shi saboda akwatin alkawarin Allah. Sai Dawuda ya tafi da murna ya kawo akwatin alkawarin Allah daga gidan Obed-edom zuwa Birnin Dawuda.
Sa'an nan na duba, sai ga Ɗan Ragon nan a tsaye a kan Dutsen Sihiyona, akwai kuma mutum dubu ɗari da dubu arba'in da huɗu tare da shi, waɗanda aka rubuta sunansa, da sunan Ubansa, a goshinsu.
Al'umman duniya za su zo, su ce, “Bari mu haura zuwa tudun Ubangiji, Zuwa Haikalin Allah na Isra'ila, Za mu koyi abin da yake so mu yi, Za mu yi tafiya a hanyar da ya zaɓa.” Koyarwar Ubangiji daga Urushalima take zuwa, Daga Sihiyona yake magana da jama'arsa.
Sulemanu kuwa ya tattara dattawan Isra'ila, da shugabannin kabilai, da shugabannin gidajen kakannin jama'ar Isra'ila, a Urushalima, domin a yi bikin fito da akwatin alkawari na Ubangiji da yake a alfarwa a birnin Dawuda, wato Sihiyona.
Sai Sulemanu ya sa dattawan Isra'ila duka, da shugabannin kabilai, da shugabannin dangi dangi na Isra'ila, su hallara a gabansa a Urushalima, domin su kawo akwatin alkawari na Ubangiji daga Sihiyona, birnin Dawuda, zuwa Haikali.
Sulemanu ya gama kai da Fir'auna, Sarkin Masar, ta wurin aure, domin ya auri 'yar Fir'auna, ya kawo ta birnin Dawuda kafin ya gama ginin gidan kansa, da Haikalin Ubangiji, da garun Urushalima.
A ran nan Dawuda ya ce, “Duk wanda zai kashe Yebusiyawa, to, sai kuma ya haura zuwa wuriyar ruwa ya fāɗa wa guragu da makafi waɗanda ran Dawuda yake ƙi.” Don haka a kan ce, “Makafi da guragu ba za su shiga Haikali ba.”
Ga shi, ina gāba da ku, ya ku mazaunan kwarin, Ya dutsen da yake a fili,’ in ji Ubangiji. ‘Ku da kuke cewa, wa zai iya gangarowa wurinku, Ko kuwa wa zai shiga wurin zamanku?
Sai Shallum ɗan Kolhoze, mai mulkin yankin Mizfa ya gyara Ƙofar Maɓuɓɓuga, ya gina ta, ya rufe ta, ya sa ƙyamarenta, da sandunan ƙarfe na kulle ƙofofinta. Ya kuma gina garun Tafkin Siluwam na gonar sarki, har zuwa matakan da suka gangaro daga Birnin Dawuda.