Sa'an nan annabin ya je wurin Sarkin Isra'ila, ya ce masa, “Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka yi tunani sosai a kan abin da za ka yi, gama da juyawar shekara Sarkin Suriya zai kawo maka yaƙi.”
Isra'ila za ta zama kamar gonar da aka girbe, aka yanke amfaninta, ta zama marar kome kamar gona a kwarin Refayawa sa'ad da aka ɗebe amfaninta. Mutane kima ne kurum za su ragu.
Daga nan iyakar ta bi ta kwarin ɗan Hinnom a wajen kudancin kafaɗar Yebus, wato Urushalima. Ta kuwa bi ta dutsen da yake shimfiɗe daura da kwarin Hinnom wajen yamma, a arewacin ƙarshen kwarin Refayawa.
Sai jarumawa uku daga cikin jarumawa talatin, suka tafi wurin Dawuda a kogon Adullam, gab da lokacin girbi. A lokacin kuwa Filistiyawa sun kafa sansani a kwarin Refayawa.