Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 5:19 - Littafi Mai Tsarki

19 Dawuda kuwa ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in yi yaƙi da Filistiyawa? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji kuwa ya ce masa, “Ka haura, gama hakika, zan ba da Filistiyawa a hannunka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

19 saboda haka Dawuda ya nemi nufin Ubangiji ya ce, “In tafi in kai wa Filistiya hari? Za ka bashe su a hannuna?” Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Je ka, gama tabbatacce zan bashe Filistiyawa a hannunka.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 5:19
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Bayan wannan sai Dawuda ya roƙi Ubangiji, ya ce, “Ko in haura in mallaki ɗaya daga cikin garuruwan Yahuza?” Ubangiji ya ce masa, “Ka haura.” Dawuda kuma ya ce, “Zuwa wane gari zan haura?” Sai Ubangiji ya ce masa, “Zuwa Hebron.”


A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da take daidai.


Sai Dawuda ya yi roƙo ga Ubangiji, ya ce, “Ko in tafi in fāɗa wa Filistiyawa da yaƙi?” Ubangiji kuwa ya ce wa Dawuda, “Tafi, ka yi yaƙi da Filistiyawa, ka ceci mutanen Kaila.”


Sai dai ya kamata ku ce, “In Ubangiji ya nufa, ya kai rai, ma yi kaza da kaza.”


Sa'an nan Sarkin Isra'ila ya tara annabawa ɗari huɗu, ya tambaye su, ya ce, “In tafi in yi yaƙi da Ramot-gileyad, ko kuwa kada in tafi?” Su kuwa suka ce masa, “Ka haura, gama Ubangiji zai ba da ita a hannunka.”


Dawuda ya kuma roƙi Ubangiji. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Kada ka haura zuwa wurinsu gaba da gaba, amma ka bi ta bayansu, ka ɓullo musu daura da itatuwan doka.


Saul kuwa ya yi tambaya ga Ubangiji, Ubangiji bai amsa masa ba, ko ta mafarkai, ko ta Urim, ko ta annabawa.


Dawuda kuma ya sāke roƙon Ubangiji. Sai Ubangiji ya amsa masa, ya ce, “Tashi, ka gangara zuwa Kaila, gama zan ba da Filistiyawa a hannunka.”


Yau ne na fara roƙar masa Allah? A'a, kada dai sarki ya zargi baransa ko gidan mahaifina duka, gama baranka bai san kome a kan wannan ba.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ