Sarautar ikonsa za ta yi ta ci gaba, Mulkinsa zai kasance da salama kullayaumin, Zai gāji sarki Dawuda, ya yi mulki a matsayinsa, Zai kafa mulkinsa a kan adalci da gaskiya, Tun daga yanzu har zuwa ƙarshen zamani. Ubangiji Mai Runduna ne ya yi niyyar aikata wannan duka.
Duk da haka yanzu sai ku yi ƙarfin hali, kai Zarubabel, da kai Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist, da dukanku mutanen ƙasar, ku kama aikin, gama ina tare da ku. Ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.
Duk inda Saul ya aiki Dawuda, sai ya tafi, ya kuma ci nasara. Saboda haka Saul ya maishe shi shugaban sojoji. Dukan jama'a da barorin Saul kuma suka ji daɗi.
Sa'an nan ya ajiye ƙungiyoyin sojojinsa a Suriya ta Dimashƙu. Suriyawa suka zama talakawan Dawuda, suka riƙa kawo masa haraji. Duk inda Dawuda ya tafi, Ubangiji yakan taimake shi.