Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 5:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Dukan kabilan Isra'ila kuwa suka zo wurin Dawuda a Hebron, suka ce, “Ga shi, mu 'yan'uwanka ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Dukan kabilar Isra’ila suka zo wurin Dawuda a Hebron suka ce, “Mu nama da jininka ne.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 5:1
13 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku ce wa Amasa, ‘Ashe, kai ba ƙashina da namana ba ne? Allah ya hukunta ni idan ba kai ne shugaban rundunar sojojina a maimakon Yowab ba.’ ”


Laban ya ce masa, “Hakika, kai ƙashina ne da namana!” Yakubu ya zauna wata guda tara da Laban.


Wato tun da yake 'ya'yan duk suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamannin haka, domin ya hallakar da mai ikon mutuwa, wato iblis, ta wurin mutuwarsa,


“Ina roƙonku, ku yi magana da shugabannin Shekem, ku ce, ‘Me ya fi muku kyau, 'ya'yan Yerubba'al, maza saba'in su yi mulkinku, ko kuwa mutum ɗaya ya yi mulkinku?’ Amma ku tuna fa ni jininku ne.”


to, kwā iya naɗa wa kanku sarki wanda Ubangiji Allahnku ya zaɓa. Sai ku naɗa wa kanku sarki daga cikin jama'arku. Kada ku naɗa wa kanku baƙo wanda ba ɗan'uwanku ba.


Joshuwa kuma ya haura tare da dukan Isra'ilawa daga Eglon zuwa Hebron, suka auka mata.


Ya ce, “Ai, ku 'yan'uwana ne, da ƙasusuwana, da namana. To, me ya sa za ku zama na ƙarshe a kan komar da sarki?


Isra'ilawa kuma suka amsa wa mutanen Yahuza, suka ce, “Muna da rabo goma a wurin sarki Dawuda fiye da ku, don me kuka raina mu? Ba mu ne muka fara maganar komowar sarki ba?” Amma maganar mutanen Yahuza ta fi ta mutanen Isra'ila zafi.


Suka ɗauki Asahel, suka tafi suka binne shi a kabarin mahaifinsa a Baitalami. Yowab kuwa da mutanensa suka bi dare farai, gari ya waye musu a Hebron.


Da haka Dawuda ya rinjayi zukatan mutanen Yahuza, suka zama ɗaya, kamar mutum guda. Sai suka aika wurin sarki, cewa, ya komo tare da dukan fādawansa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ