Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 3:31 - Littafi Mai Tsarki

31 Dawuda kuwa ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku kyakketa tufafinku, ku sa tsummoki, ku yi makoki domin Abner.” Sarki Dawuda kuwa ya bi bayan makara.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

31 Sa’an nan Dawuda ya ce wa Yowab da dukan mutanen da suke tare da shi, “Ku yayyage rigunarku, ku sa tsummoki, ku yi tafiya kuna kuka a gaban Abner.” Sarki Dawuda kansa ya bi masu ɗauke da gawar daga baya.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 3:31
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sai Yakubu ya kyakkece rigunansa, ya yi ɗamara da majayi, ya yi kukan ɗansa har kwanaki masu yawa.


Sai Dawuda ya yayyage tufafinsa. Dukan mutanen da suke tare da shi kuma suka yayyage nasu.


Kashegari sai ga wani mutum ya zo daga sansanin Saul, da tufafinsa a yayyage, da ƙura kuma a kansa. Da ya zo wurin Dawuda sai ya fāɗi ƙasa, ya yi gaisuwa.


Sa'ad da ya gan ta sai ya yayyage tufafinsa, ya ce, “Kaito, 'yata, kin karya mini gwiwa, kin zamar mini babban dalilin wahala. Na riga na yi wa'adi ga Ubangiji, ba kuwa zan iya warware shi ba.”


Sai Joshuwa ya yayyage tufafinsa, ya faɗi rubda ciki a gaban akwatin Ubangiji har yamma. Shi da dattawan Isra'ila, suka zuba ƙura a bisa kansu.


Sa'an nan ya matso, ya taɓa makarar, masu ɗauka kuma suka tsaya cik. Sai Yesu ya ce, “Samari, na ce maka ka tashi.”


Da sarki Hezekiya ya ji wannan magana, sai ya kyakketa tufafinsa, ya sa rigar makoki, sa'an nan ya shiga Haikalin Ubangiji.


Sa'ad da Ra'ubainu ya koma a wajen rijiya, da bai ga Yusufu a cikin rijiyar ba, sai ya kyakkece tufafinsa,


Zan kuma bai wa mashaidana biyu iko su yi annabci kwana dubu da metan da sittin, suna a saye da tsummoki.”


Fadawansa suka je suka ce masa, “Mun ji an ce sarakunan Isra'ila masu jinƙai ne, bari mu sa tufafin makoki, mu ɗaura igiyoyi a wuyanmu, sa'an nan mu tafi wurin Sarkin Isra'ila, watakila zai bar ka da rai.”


Da Ahab ya ji wannan magana, sai ya yage tufafinsa, ya sa na makoki, ya yi azumi, ya kwanta a tsummokin makoki, ya tashi yana tafiya a hankali.


Sai ya aiki Eliyakim wakilin gidan sarki, da Shebna magatakarda, da manyan firistoci, saye da tufafin makoki zuwa wurin annabi Ishaya, ɗan Amoz,


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ