Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 3:29 - Littafi Mai Tsarki

29 Allah ya sa alhakin jinin ya faɗa kan Yowab da dukan gidan ubansa. Ya sa kada a rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko wanda yake dogara sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko wanda ba shi da abinci, a gidan Yowab.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

29 Alhakin jininsa yă kasance a kan Yowab da kuma a kan dukan iyalin mahaifinsa! Kada gidan Yowab yă rasa mai ɗiga, ko kuturu, ko mai jingina ga sanda, ko wanda aka kashe da takobi, ko kuma wanda ba shi da abinci.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 3:29
18 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Dawuda kuwa ya ce, “Alhakin jininka yana bisa kanka tun da yake da bakinka ka ce, ‘Ni ne na kashe wanda Ubangiji ya keɓe.’ ”


Don mutane sun zub da jinin tsarkaka da na annabawa, Ga shi kuwa, ka ba su jini su sha. Sakamakonsu ke nan!”


Da mutanen garin suka ga mugun ƙwaron nan a makale a hannun Bulus, suka ce wa juna, “Lalle mutumin nan mai kisankai ne, kun ga ko da yake ya tsira daga bahar, duk da haka alhaki yana binsa sai ya mutu.”


Saboda haka kuturtar Na'aman za ta kama ka, kai da zuriyarka har abada.” Haka kuwa ya fita a wurinsa kuturu, fari fat kamar auduga.


Na'aman kuwa, shugaban sojojin Sarkin Suriya, shi babba ne mai farin jini ƙwarai a wurin ubangidansa, domin ta wurinsa ne Ubangiji ya ba Suriyawa nasara. Shi mutum ne ƙaƙƙarfan jarumi, amma kuma kuturu ne.


Wannan ya faru domin a ɗauki fansar jinin, 'ya'yan Yerubba'al, maza, su saba'in, a kan Abimelek ɗan'uwansu, wanda ya kashe su, da kuma a kan shugabannin Shekem, waɗanda suka taimake shi ya kashe 'yan'uwansa.


domin jama'ar Isra'ila. Duk lokacin da wani namiji yake ɗiga daga al'aurarsa, ƙazantacce ne.


Sai dukan dattawan garin da ya fi kusa da gawar su wanke hannuwansu a bisa karsanar da aka karya wuyanta a kwarin.


Daga baya sa'ad da Dawuda ya ji, sai ya ce, “Ni da mulkina baratattu ne a gaban Ubangiji daga alhakin jinin Abner ɗan Ner har abada.


Ubangiji ya sāka maka saboda alhakin jinin gidan Saul, wanda ka hau gadon sarautarsa. Yanzu Ubangiji ya ba da sarautar ga Absalom, ɗanka. Duba, masifa ta auko maka, gama kai mai kisankai ne.”


idan mutumin ya sāke tashi ya yi tafiya ko da yana dogarawa da sanda, wanda ya buge shi zai kuɓuta, sai dai zai biya diyyar lokacin da ya ɓāta masa, ya kuma lura da shi har ya warke sarai.


Saboda haka kada ku ƙazantar da ƙasar da kuke zaune a ciki, gama jini yakan ƙazantar da ƙasa. Ba wata kafara da za a yi don ƙasar da aka zubar da jini a cikinta, sai dai da jinin wanda ya zubar da jinin.


Zan gode wa Ubangiji saboda adalcinsa, Zan raira yabbai ga Ubangiji, Maɗaukaki.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ