2 Samaʼila 24:16 - Littafi Mai Tsarki16 Sa'ad da mala'ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima don ya hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala'ikan da yake hallakar da mutanen, “Ya isa, ka janye hannunka.” Mala'ikan ya tsaya kusa da masussukar Arauna Bayebuse. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202016 Da mala’ikan Ubangiji ya miƙa hannunsa wajen Urushalima, don yă hallaka ta, sai Ubangiji ya tsai da masifar, ya ce wa mala’ikan da yake wahal da mutane, “Ya isa, ka janye hannunka.” A lokacin kuwa Mala’ikan Ubangiji yana tsaye a masussukar Arauna, mutumin Yebus. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Ubangiji kuwa ya aiki mala'ika wanda ya karkashe manyan jarumawa, da sarakunan yaƙi, da shugabanni, da kowane riƙaƙƙen soja, da sarkin yaƙi da yake a sansanin Sarkin Assuriya. Sai ya koma ƙasarsa cike da kunya. Sa'ad da ya shiga gidan gunkinsa, sai waɗansu daga cikin 'ya'yan cikinsa suka kashe shi da takobi.