Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 24:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kuwa kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gabanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu sai ka yi tunani, ka faɗi irin amsar da zan mayar wa Ubangiji da ya aiko ni.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Sai Gad ya zo wurin Dawuda ya ce masa, “Kana so a yi yunwa shekara uku a ƙasarka? Ko kana so ka yi ta gudu a gaban abokan gābanka har wata uku? Ko kuwa ka fi so a yi annoba kwana uku a ƙasarka? Yanzu, sai ka yi tunani, ka yanke shawarar game da amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 24:13
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

ko shekara uku na yunwa, ko kuwa ka sha ɗibga a hannun maƙiyanka har wata uku, maƙiyanka su yi ta fafararka, ko kwana uku na takobin Ubangiji, wato annoba ke nan da zai aukar wa ƙasar, mala'ikan Ubangiji zai yi ta hallakarwa ko'ina a ƙasar Isra'ila. Yanzu fa, sai ka yi tunani, ka ba ni amsar da zan mayar wa wanda ya aiko ni.”


A zamanin Dawuda aka yi yunwa shekara uku bi da bi. Dawuda kuwa ya roƙi Ubangiji. Sai Ubangiji ya ce masa, “Akwai alhakin jini a kan Saul da gidansa, domin ya kashe Gibeyonawa.”


Zan sa a kawo muku yaƙi saboda karya alkawarina da kuka yi. Idan kuwa kun tattaru a cikin biranenku, sai in aukar muku da masifa, in bashe ku ga maƙiyanku.


Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra'ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa'ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar.


“Ɗan mutum, sa'ad da wata ƙasa ta yi mini laifi na rashin aminci, ni kuwa na miƙa hannuna gāba da ita, na toshe hanyar abincinta, na aika mata da yunwa, na kashe mata mutum duk da dabba,


Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku.


Ubangiji zai bugi gwiwoyinku da ƙafafunku da marurai tun daga tafin ƙafarku har zuwa ƙoƙwan kanku.


Ubangiji zai buge ku da marurai irin na Masar, da basur, da ƙazwa, da ƙaiƙayi waɗanda ba za su warke ba.


“Ubangiji zai sa abokan gabanku su rinjaye ku cikin yaƙi. Ta hanya guda za ku auka musu, amma ta hanyoyi bakwai za ku gudu daga gabansu. Za ku zama abin ƙi ga dukan mulkokin duniya.


Ubangiji zai buge ku da ciwon fuka, da zazzaɓi, da ciwon kumburi, da zafi mai tsanani, da fari, da burtuntuna, da fumfuna. Waɗannan za su yi ta damunku har ku lalace.


Za ku ɓarnatar da ƙarfinku a banza gama ƙasarku ba za ta ba da amfaninta ba, itatuwan ƙasar kuma ba za su ba da 'ya'ya ba.


Ko annobar da take aukowa da dare, Ko mugayen da suke kisa da tsakar rana.


“Tafi ka faɗa wa Dawuda na ba shi abu uku don ya zaɓi ɗaya wanda za a yi masa daga cikinsu.”


Kwana bakwai suka cika bayan da Ubangiji ya bugi Kogin Nilu.


Yanzu sai ki yi tunani, ki san abin da ya kamata ki yi, gama ana niyyar yi wa maigida da dukan gidansa ɓarna. Ga shi, maigida yana da mugun hali, ba zai ji kowa ba!”


Elisha kuwa ya ce wa matar da ya ta da ɗanta daga matattu, “Ki tashi, ke da gidanki, ki zauna duk inda kika samu, gama Ubangiji ya sa a yi yunwa a ƙasar har shekara bakwai.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ