“Kai ɗan mutum, kada ka ji tsoronsu, kada kuma ka ji tsoron maganganunsu, ko da ya ke ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya sun kewaye ka, kana kuma zaune tare da kunamai. Kada ka ji tsoron maganganunsu ko ka karai saboda irin kallon da za su yi maka, gama su 'yan tawaye ne.
Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra'ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.”
Yanzu sai ki yi tunani, ki san abin da ya kamata ki yi, gama ana niyyar yi wa maigida da dukan gidansa ɓarna. Ga shi, maigida yana da mugun hali, ba zai ji kowa ba!”
Mutumin kirkinsu kamar ƙaya yake, Mai gaskiyarsu kuwa kamar shingen ƙaya yake. Ranar da kuka sa mai tsaro, A ran nan za a aukar muku da hukunci. Yanzu ruɗewarku ta zo,