Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 23:20 - Littafi Mai Tsarki

20 Benaiya ɗan Yehoyada, mutumin Kabzeyel, jarumi ne. Ya yi manyan ayyuka. Ya kashe ƙwararrun jarumawa biyu na Mowab. Wata rana kuma da aka yi dusar ƙanƙara, sai ya tafi ya kashe zaki a kogo.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

20 Benahiya, ɗan Yehohiyada mutumin Kabzeyel shi ma jarumi ne sosai, ya yi nasarori masu yawa. Ya bugi ƙwararrun jarumawan Mowab guda biyu. Ya kuma shiga rami wata ranar da ake ƙanƙara, ya kashe zaki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 23:20
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Yowab shi ne shugaban dukan sojojin Isra'ila, Benaiya, ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato masu tsaro.


Benaiya ɗan Yehoyada, shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. 'Yan'yan Dawuda, maza, suka zama mataimakansa.


Biranen jama'ar Yahuza da suke can kudu sosai wajen iyakar Edom, su ne Kabzeyel, da Eder, da Yagur,


Sa'an nan sarki ya umarci Benaiya ɗan Yehoyada, ya tafi, ya kashe Shimai. Yanzu sarauta ta tabbata a hannun Sulemanu.


Saboda haka sai Zadok, firist, da annabi Natan, da Benaiya ɗan Yehoyada, da masu tsaron lafiyar sarki, suka tafi, suka sa Sulemanu ya hau alfadarin sarki Dawuda. Suka kuma kai shi Gihon.


Amma ni da Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da ɗanka Sulemanu, bai gayyace mu ba.


Amma Zadok, firist, da Benaiya ɗan Yehoyada, da annabi Natan, da Shimai, da Reyi, da masu tsaron lafiyar Dawuda, ba su goyi bayan Adonija ba.


Sarakunan Edom suka tsorata, Shugabannin Mowab suna rawar jiki, Dukan mazaunan Kan'ana sun narke.


Waɗannan su ne sunayen shahararru, ƙwararrun mayaƙa daga kabilar Gad, waɗanda suka haɗa kai da sojojin Dawuda, sa'ad da yake a kagara a hamada. Su gwanayen yaƙi da garkuwa da mashi ne. Fuskokinsu kamar na zakoki, saurinsu kamar bareyi a kan dutse.


“Saul da Jonatan ƙaunatattu ne, suna da bansha'awa, A raye suna tare, haka kuma a mace suna tare. Sun fi gaggafa sauri, Sun fi zaki ƙarfi.


Benaiya ɗan Yehoyada shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa, wato matsara. 'Ya'yan Dawuda, maza, su ne manyan ma'aikata na kusa da shi.


Shi ya fi shahara daga cikin su talatin ɗin, don haka ya zama shugabansu, amma bai kai su uku ɗin can ba.


Ya kuma kashe wani Bamasare mai cika fuska. Bamasaren yana da māshi a hannunsa, amma Benaiya ya tafi wurinsa da sanda, ya fizge mashin daga hannun Bamasaren, ya kashe shi da māshin.


Abubuwan da Benaiya, ɗan Yehoyada ya yi ke nan. Da haka ya samar wa kansa suna tare da jarumawan nan talatin.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ