6 Mutuwa ta ɗaure ni da igiyoyinta da ƙarfi, Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
6 Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe ni; tarkuna kuma suka auka mini.
Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam, Razanar kabari ta auka mini, Na cika da tsoro da alhini.
Amma Allah ya tashe shi bayan ya ɓalle masa ƙangin mutuwa, domin ba shi yiwuwa mutuwa ta riƙe shi.
ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare ka, ya Ubangiji, Ka a kuwa amsa mini. Daga can cikin lahira na yi kira, Ka kuwa ji muryata.
Kana so ka kauce wa mutuwa? To, tsoron Ubangiji shi ne maɓuɓɓugar rai.
Koyarwar masu hikima maɓuɓɓugar rai ce, za ta taimake ka ka kuɓuta sa'ad da ranka yake cikin hatsari.
Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi.
Masu girmankai sun kafa mini tarko, Sun shimfiɗa ragar igiya, Sun kuma kakkafa tarkuna a hanya don su kama ni.
Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta, Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
Amma idan aka ɗaure su da sarƙoƙi, Da kuma igiyar wahala,
“Sa'ad da kuka ga rundunonin yaƙi sun kewaye Urushalima, sa'an nan ku tabbata ana kusan ribɗe ta.