Shi yake kiyaye ni, Shi yake kāre ni, Shi ne mafakata da Mai Cetona, Wanda nake dogara gare shi Don samun zaman lafiya. Shi ne ya ɗora ni a kan al'ummai.
Sai ga Bahabashe ya iso, ya ce, “Abishirinka, ya ubangijina, sarki, gama a wannan rana ta yau Ubangiji ya cece ka daga hannun waɗanda suka tayar maka.”
Sa'ad da Dawuda ya ji Nabal ya mutu, sai ya ce, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji wanda ya sāka mini a kan irin rainin da Nabal ya yi mini. Ya kuma hana ni aikata mugunta. Ya ɗora wa Nabal muguntarsa a kansa.” Sa'an nan Dawuda ya aika, ya nemi Abigail ta zama matarsa.
Suka kai wa Dawuda kan Ish-boshet a Hebron. Suka ce wa sarki Dawuda, “Ga kan Ish-boshet ɗan maƙiyinka, Saul, wanda ya nemi ranka. Ubangiji ya rama wa sarki a kan Saul da zuriyarsa yau.”