41 Ka sa abokan gābana su gudu daga gabana, Na hallaka waɗanda suke ƙina.
41 Ka sa abokan gābana suka juya a guje, na kuwa hallaka maƙiyina.
“Zan aiki razanata a gabanku, in sa mutanen da za ku gamu da su su ruɗe. Zan sa maƙiyanku duka su ba ku baya, su sheƙa a guje.
Da suka kawo sarakunan a wurin Joshuwa, sai Joshuwa ya kirawo dukan Isra'ilawa, sa'an nan ya ce wa shugabannin mayaƙa, waɗanda suka tafi tare da shi, “Ku matso kusa, ku taka wuyan sarakunan nan.” Suka kuwa zo kusa, suka taka wuyansu.
Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”
Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu.
“Yahuza, 'yan'uwanka za su yabe ka, Za ka shaƙe wuyan maƙiyanka, 'Yan'uwanka za su rusuna a gabanka.