37 Ka hana a kama ni, Ban kuwa taɓa faɗuwa ba.
37 Ka fadada hanya a ƙarƙashina domin kada idon ƙafana yă juya.
Idan ka yi tafiya da hikima ba abin da zai tsare maka hanya, sa'ad da kake gudu ba za ka yi tuntuɓe ba.
Ina tafiya a kan tafarkinka kullum, Ban kuwa kauce ba.
“Zai kiyaye rayukan amintattun mutanensa, Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu, Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.
Ba zai bar ka ka fāɗi ba, Makiyayinka, ba zai yi barci ba!
Na ce, “Ina kan fāɗuwa,” Amma, ya Ubangiji, madawwamiyar ƙaunarka ta riƙe ni.
Ka tsare ni, ba a kama ni ba, Ban kuwa taɓa fāɗuwa ba.
Ka amsa mini sa'ad da na yi kira, Ya Allah, madogarata! Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona. Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!
Ya taimake ni ya fisshe ni daga hatsari, Ya cece ni domin yana jin daɗina.