36 “Ya Ubangiji, ka kiyaye ni, ka cece ni, Taimakonka ya sa na zama babba.
36 Ka ba ni garkuwar nasararka; ka sauko don ka sa in sami girma.
Banda waɗannan kuma, ku ɗauki garkuwar bangaskiya, wadda za ku iya kashe dukan kiban wutar Mugun nan da ita.
Ubangiji ya ba ku 'ya'ya, Ku da zuriyarku.
Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
Ya Ubangiji ka kiyaye ni, ka cece ni, Na zama babban mutum saboda kana lura da ni, Ikonka kuma ya kiyaye lafiyata.
hakika zan sa maka albarka, zan riɓaɓɓanya zuriyarka kamar taurarin sama, kamar yashi kuma a gāɓar teku. Zuriyarka za su mallaki ƙofar maƙiyanka,
Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”
Zan kuwa maishe ka al'umma mai girma, zan sa maka albarka, in sa ka ka yi suna, domin ka zama sanadin albarka.
Ku kuma ɗauki kwalkwalin ceto, da takobin Ruhu, wato Maganar Allah,