sa'an nan ne za ku yi murna cikin Ubangiji, zan sa ku a kan maɗaukakan wurare na duniya. Zan kuma ciyar da ku da gādon mahaifinku Yakubu, ni Ubangiji na faɗa.”
Wannan ita ce maganar Dawuda ta ƙarshe. Dawuda ɗan Yesse, shi ne mutumin da Allah ya ɗaukaka, wanda Allah na Yakubu ya zaɓa ya zama sarki, wanda kuma ya shirya waƙoƙin Isra'ila. Dawuda ya ce,