Ya jama'ata, kada ku ji tsoro! Kun sani tun daga zamanin dā can, har zuwa yanzu, Na faɗa tun da wuri abin da zai faru. Ku ne kuwa shaiduna! Ko akwai wani Allah? Ko akwai wani Allah mai iko da ban taɓa jin labarinsa ba?”
Ku zo ku gabatar da matsalarku a ɗakin shari'a, Bari waɗanda aka kai ƙara su yi shawara da juna. Wane ne ya faɗi abin da zai faru, Ya kuma yi annabci tuntuni? Ashe, ba ni ba ne, Ubangiji, Allah wanda ya ceci mutanensa? Ba wani Allah sai ni.
Ubangiji, wanda yake mulkin Isra'ila, ya kuma fanshe su, Ubangiji Mai Runduna, yake faɗar wannan, “Ni ne farko, da ƙarshe, Allah Makaɗaici, Ba wani Allah sai ni.