A lokacin da Abram yake da shekara tasa'in da tara Ubangiji ya bayyana gare shi, ya ce masa, “Ni ne Allah Mai Iko Dukka. Ka yi mini biyayya, ka zama kamili.
Saboda haka, tun da taron shaidu masu ɗumbun yawa suka kewaye mu haka, sai mu ma mu yar da dukkan abin da ya nauyaya mana, da kuma zunubin da ya ɗafe mana, mu kuma yi tseren nan da yake gabanmu tare da jimiri,
Da yake muna tsoron Ubangiji, shi ya sa muke ƙoƙarin rinjayar mutane. Yadda muke kuwa, ai, sananne ne ga Allah, muna fata ku ma haka abin yake a lamirinku.
Ubangiji shi ne makiyayinmu, sarkinmu mai daraja, Yakan sa mana albarka, da alheri, da daraja, Ba ya hana kowane abu mai kyau ga waɗanda suke aikata abin da yake daidai.
Amma a yanzu ya sulhunta ku ta hanyar jikinsa na mutuntaka, wato, ta wurin mutuwarsa, domin ya miƙa ku tsarkakakku, marasa aibu, marasa abin zargi kuma a gabansa.