Shi yake kiyaye ni, Shi yake kāre ni, Shi ne mafakata da Mai Cetona, Wanda nake dogara gare shi Don samun zaman lafiya. Shi ne ya ɗora ni a kan al'ummai.
“Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi, Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
Saul da mutanensa suka tafi neman Dawuda. Da Dawuda ya ji labari, sai ya sauka daga dutsen ya zauna a can jejin Mawon. Da Saul ya ji, sai ya bi Dawuda zuwa jejin Mawon.