Ko da hanyan nan ta bi ta tsakiyar duhu na mutuwa, Ba zan ji tsoro ba, ya Ubangiji, Gama kana tare da ni! Sandanka na makiyayi da kerenka Suna kiyaye lafiyata.
Ku duka da kuke tsoron Ubangiji, Kuna kuma biyayya da kalmomin bawansa, Zai yiwu hanyar da kuke bi ta yi duhu ƙwarai, Amma ku dogara ga Ubangiji, ku jingina ga Allahnku.
Mutanenmu da suka mutu za su sāke rayuwa! Jikunansu za su sāke rayuwa! Dukan waɗanda suke kwance cikin kaburburansu Za su farka, su yi waƙa don farin ciki! Kamar laimar raɓa wanda yake wartsakar da duniya, Haka Ubangiji zai rayar da waɗanda suka daɗe da mutuwa.