Sa'ad da kuke bi ta cikin ruwa mai zurfi, Zan kasance tare da ku, Wahala ba za ta fi ƙarfinku ba. Sa'ad da kuke bi ta cikin wuta, ba za ku ƙuna ba, Wuyar da ta same ku ba za ta cuce ku ba.
Da jaririn ya yi girma sai ta kai shi wurin Gimbiyar. Yaro kuwa ya zama tallafinta. Ta raɗa masa suna Musa, gama ta ce, “Domin na tsamo shi daga cikin ruwa.”