Ɗaukakar Ubangiji kuwa ta tashi daga kan siffar kerubobi inda take zaune zuwa bakin ƙofar Haikalin. Sai Ubangiji ya kira mutumin da yake saye da rigar lilin, wanda yake rataye da gafaka.
Sai suka aika zuwa Shilo aka kawo akwatin alkawarin Ubangiji Mai Runduna, wanda yake zaune a tsakanin kerubobi. 'Ya'yan nan na Eli, maza guda biyu, wato Hofni da Finehas, suna tare da akwatin alkawarin.
Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.
Sai ya tafi tare da su duka zuwa Kiriyat-yeyarim domin ya kawo akwatin Alkawarin Allah, wanda ake kira da sunan Ubangiji Mai Runduna wanda yake zaune a tsakanin kerubobin.