2 Samaʼila 21:10 - Littafi Mai Tsarki10 Rizfa kuwa, 'yar Aiya, ta ɗauki algarara ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutsen. Ta zauna a wurin tun daga farkon kaka har zubar ruwan damuna da ya bugi gawawwakin. Ba ta bar tsuntsaye su sauka a kansu da rana ba, ko namomin jeji da dare. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202010 Rizfa ’yar Aiya ta ɗauki tsumma ta yi wa kanta shimfiɗa a kan dutse. Tun daga farkon girbi har ruwa damina ya sauko a kan gawawwakin, ba tă yarda tsuntsayen sama su taɓa su da rana ko mugayen namun jeji da dare ba. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |