Ya amsa, ya ce, “Wa ya naɗa ka sarki ko alƙali a bisanmu? So kake ka kashe ni kamar yadda ka kashe Bamasaren?” Sai Musa ya tsorata, ya ce, “Assha, ashe, an san al'amarin!”
Mawaƙa, 'ya'yan Asaf, maza, suna wurinsu bisa ga umarnin Dawuda, da Asaf, da Heman, da kuma Yedutun maigani na sarki, matsaran ƙofofi kuma suna a kowace ƙofa, ba lalle sai su bar wurin hidimarsu gama 'yan'uwansu Lawiyawa sun shirya musu nasu.
Fir'auna kuwa ya sa wa Yusufu suna, Zafenat-faneya. Ya kuma aurar masa da Asenat 'yar Fotifera, firist na On. Yusufu kuwa ya fita rangadin ƙasar Masar.
A zamanin Dawuda aka yi yunwa shekara uku bi da bi. Dawuda kuwa ya roƙi Ubangiji. Sai Ubangiji ya ce masa, “Akwai alhakin jini a kan Saul da gidansa, domin ya kashe Gibeyonawa.”
(Yayir na zuriyar Manassa ya karɓi dukan yankin ƙasar Argob a Bashan har zuwa iyakar Geshurawa da Ma'akatiyawa. Sai ya kira ƙauyukan wurin da sunansa, Hawot-yayir.)