Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 20:22 - Littafi Mai Tsarki

22 Macen ta tafi wurin dukan mutanen garin da wayo. Su kuwa suka yanke kan Sheba, ɗan Bikri, suka jefa wa Yowab. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, suka janye daga garin. Kowa ya tafi gidansa. Yowab kuma ya koma Urushalima wurin sarki.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

22 Sa’an nan matar ta tafi wurin dukan mutane da shawararta mai hikima, sai suka datse kan Sheba ɗan Bikri suka jefa wa Yowab. Saboda haka sai ya busa ƙaho, mutanensa kuwa suka watse daga birnin, kowa ya koma gidansa. Yowab kuma ya koma wurin sarki a Urushalima.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 20:22
10 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Abin da hikima take iya yi wa mutum ɗaya ya fi abin da masu mulki goma za su yi wa birni.


Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra'ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.”


Don me mutane suke aikata laifofi a natse? Domin ba a hukunta laifofi nan da nan.


Sai wata mace mai hikima ta yi kira daga cikin garin, ta ce, “Ji mana! A faɗa wa Yowab, ya zo nan, ina so in yi magana da shi.”


Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, sojoji suka komo daga runtumar Isra'ilawa. Yowab ya tsai da su.


Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, dukan mutanensa kuwa suka tsaya, ba su ƙara runtumar mutanen Isra'ila ba, ba wanda kuma ya yaƙi wani.


Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra'ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ