Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 20:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Da can akwai wani mutumin banza, ana ce da shi Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Biliyaminu. Shi kuwa ya busa ƙaho, ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu kuwa da gado wurin ɗan Yesse. Ya Isra'ilawa, kowa ya gudu zuwa alfarwarsa.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Akwai wani mai tā-da-na-zaune-tsaye, sunansa Sheba, ɗan Bikri, daga kabilar Benyamin, a wurin. Sai ya busa ƙaho, ya yi ihu ya ce, “Ba mu da rabo a wurin Dawuda, ba mu da sashe a wurin ɗan Yesse! Kowa yă nufi tentinsa, ya Isra’ila!”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 20:1
31 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Da mutanen Isra'ila suka ga sarki ya ƙi jin roƙonsu, sai suka yi ihu, suna cewa, “A yi ƙasa da Dawuda da iyalinsa. Me suka taɓa yi mana? Mazajen Isra'ila, bari duka mu tafi gida! Mu bar Rehobowam ya lura da kansa!” Jama'ar Isra'ila fa suka tayar,


Da Isra'ilawa duka suka ga sarki bai saurare su ba, jama'ar kuwa suka amsa wa sarkin, suka ce, “Wane rabo muke da shi a wurin Dawuda? Ba mu da gādo a wurin ɗan Yesse. Kowa ya tafi alfarwarsa, ya ku Isra'ilawa. Ku bar Rehobowam ya lura da gidansa.” Isra'ilawa duka kowa ya tafi alfarwarsa.


Waɗannan maƙiya nawa kuwa, da ba sa so in yi mulki a kansu, ku kawo su nan a kashe su a gabana.’ ”


Amma mutanensa suka ƙi shi, har suka aiki jakadu a bayansa, cewa ba sa so ya yi mulki a kansu.


Kamar yadda gawayi yake ga garwashin wuta, itace kuma ga wuta, haka mai gardama yake ga jayayya.


Kada ka yi garajen kai ƙara a majalisa. Idan wani mashaidi ya nuna kai kake da kuskure, me za ka yi?


Mutumin kirki yakan sha wahala da yawa, Amma Ubangiji yakan cece shi daga cikinsu duka.


Ka zo, ya Ubangiji, Ka yi yaƙi da maƙiyana, ka yi nasara da su! Ka cece ni da takobinka daga mugaye,


Rehobowam ya nemi shawara a gun dattawan da suke tare da tsohonsa Sulemanu, sa'ad da yake da rai, ya ce, “Wace shawara za ku ba ni don in amsa wa jama'ar nan?”


Amma marasa Allah suna kama da ƙayayuwan da aka zubar,


Amma Absalom ya aiki manzanni a asirce cikin dukan kabilan Isra'ila a faɗa musu haka, “Da zarar kun ji an busa ƙaho, sai ku ce, ‘Absalom shi ne sarki, yana Hebron.’ ”


Sai dukan mugaye da marasa kirki daga cikin mutanen da suka tafi tare da Dawuda suka ce, “Tun da yake ba su tafi tare da mu ba, ba za mu ba su kome daga cikin ganimar da muka ƙwato ba, sai dai kowane mutum ya ɗauki matarsa da 'ya'yansa ya tafi.”


'Ya'yan Eli, maza kuwa, ba su da kirki, ba su kula da Ubangiji ba,


Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”


Da ya isa can sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Ifraimu. Jama'ar Isra'ila kuwa suka gangara tare da shi daga ƙasar tudu. Yana kan gaba.


Bitrus ya ce masa, “Wane ni! Ai, ba za ka wanke mini ƙafa ba har abada!” Yesu ya amsa masa ya ce, “In ban wanke maka ba, ba ka da rabo a gare ni.”


'Ya'yan Biliyaminu, maza, su ne Bela, da Beker, da Ashbel, da Gera, da Na'aman, da Ahiram, da Rosh, da Muffim, da Huffim, da Adar.


Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000) daga Isra'ila, dubu biyu (2,000) su zauna tare da shi a Mikmash da ƙasar tuddai ta Betel, dubu ɗaya (1,000) kuma su zauna tare da Jonatan a Gibeya ta Biliyaminu, sauran jama'a kuwa ya sallame su, su koma gida, kowa zuwa alfarwarsa.


Shimai ya yi ta zagi, yana cewa, “Tafi, tafi, kai mai kisankai, sakarai.


Suka ɗauki gawar Absalom, suka jefa ta cikin wani rami mai zurfi a kurmin, suka tula tsibin duwatsu a kanta. Dukan Isra'ilawa kowa ya tsere zuwa gidansa.


Sai dukan Isra'ilawa suka janye jiki daga wurin Dawuda, suka bi Sheba, ɗan Bikri, amma mutanen Yahuza suka manne wa sarki tun daga Urdun har zuwa Urushalima.


Macen ta tafi wurin dukan mutanen garin da wayo. Su kuwa suka yanke kan Sheba, ɗan Bikri, suka jefa wa Yowab. Sa'an nan Yowab ya busa ƙaho, suka janye daga garin. Kowa ya tafi gidansa. Yowab kuma ya koma Urushalima wurin sarki.


A kuma sa 'yan iska guda biyu, su yi ta zarginsa, su riƙa cewa, ‘Nabot ya zagi Allah da sarki.’ Sa'an nan ku tafi da shi, ku jajjefe shi da duwatsu har ya mutu.”


Rut ta tafi wata gona, tana bin bayan masu girbi, tana kala. Ta yi sa'a kuwa ta fāɗa a gonar Bo'aza, dangin Elimelek.


Dawuda kuma ya ce wa Abishai da dukan fādawansa, “Ga shi ma, ɗana na cikina yana neman raina, balle wannan mutumin Biliyaminu! Ku bar shi ya yi ta zagi, gama Ubangiji ne ya umarce shi.


Ai, in mulki ya rabu a kan gāba, wannan mulki ba zai ɗore ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ