Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 2:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Yanzu sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Saul shugabanku ya rasu, mutanen Yahuza kuwa sun naɗa ni sarkinsu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Yanzu fa, sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Shawulu sarkinku ya mutu, gidan Yahuda kuwa sun naɗa ni sarki a kansu.”

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 2:7
12 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

A ƙarshe kuma, ku ƙarfafa ga Ubangiji, ga ƙarfin ikonsa.


Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama'armu da biranen Allahnmu. Ubangiji ya yi abin da ya gamshe shi.”


sai dukan jarumawa suka tashi, suka yi tafiya dukan dare. Suka ɗauko gawar Saul da gawawwakin 'ya'yansa daga kan garun Bet-sheyan. Da suka zo Yabesh sai suka ƙone su a can.


Sa'ad da Isra'ilawan da suke a wancan hayi na kwarin da waɗanda suke a wancan hayin Urdun suka ga mayaƙan Isra'ila sun gudu, Saul kuma da 'ya'yansa sun mutu, sai suka bar garuruwansu, suka gudu. Filistiyawa kuwa suka zo suka zauna a cikinsu.


Ya ku Filistiyawa, ku yi ƙarfin hali, ku yi jaruntaka don kada ku zama bayin Ibraniyawa kamar yadda suka zama bayinku, ku yi jaruntaka ku yi yaƙi.”


Bayan waɗannan al'amura, maganar Ubangiji ta zo ga Abram cikin wahayi cewa, “Abram, kada ka ji tsoro, ni ne garkuwarka, kana da lada mai yawa.”


Ku zauna a faɗake, ku dāge ga bangaskiyarku, ku yi ƙwazo, ku yi ƙarfi.


Ubangiji ya nuna muku ƙaunarsa da amincinsa. Ni kuwa zan yi muku alheri saboda abin da kuka yi.


Abner kuwa ɗan Ner, sarkin yaƙin Saul, ya tsere da Ish-boshet, ɗan Saul, zuwa Mahanayim.


Na kuma faɗa musu yadda Allah yana tare da ni, ya kuma taimake ni, da maganar da sarki ya faɗa mini. Sai suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Suka himmatu su yi wannan aiki nagari.


Sai dukan dattawan Isra'ila suka tafi wurin sarki Dawuda a Hebron, shi kuwa ya yi alkawari da su a gaban Ubangiji. Su kuwa suka naɗa shi Sarkin Isra'ila duka.


Sa'an nan ya fito da ɗan sarki, ya sa kambin sarauta a kansa, ya kuma ba shi dokokin. Suka naɗa shi, suka zuba masa man naɗawa, sa'an nan suka yi tāfi suna cewa, “Ran sarki ya daɗe.”


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ