Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




2 Samaʼila 2:18 - Littafi Mai Tsarki

18 'Ya'yan Zeruya, maza, su uku suna nan, wato Yowab, da Abishai, da Asahel. Asahel maguji ne kamar barewa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

18 ’Ya’yan Zeruhiya, maza uku sun kasance a can. Su ne, Yowab, Abishai da Asahel. To, Asahel mai gudu ne kamar barewa.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




2 Samaʼila 2:18
19 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Waɗannan su ne sunayen shahararru, ƙwararrun mayaƙa daga kabilar Gad, waɗanda suka haɗa kai da sojojin Dawuda, sa'ad da yake a kagara a hamada. Su gwanayen yaƙi da garkuwa da mashi ne. Fuskokinsu kamar na zakoki, saurinsu kamar bareyi a kan dutse.


Ubangiji Allah shi ne ƙarfina, Ya sa ƙafafuna su zama kamar na bareyi, Ya kuma sa ni in yi tafiya a cikin maɗaukakan wurare.


Ya ƙaunataccena, ka zo wurina da sauri, kamar batsiya, Ko sagarin kishimi a kan duwatsu inda kayan yaji yake tsirowa.


Har hurowar iskar safiya, Sa'ad da duhu ya kawu. Komo ya ƙaunataccena, yi kamar barewa, Kamar sagarin kishimi a kan duwatsu.


Yana sa in tabbata lafiya nake tafiya, kamar barewa. Yana kiyaye ni lafiya a kan duwatsu.


Ko masu saurin gudu ma ba za su tsere ba, Ƙarfafa za su zama kumamai, Sojoji kuma ba za su iya ceton kansu ba.


Na gane wani abu kuma, ashe, a duniyan nan ba kullum maguji ne yake cin tsere ba, ba kullum jarumi ne yake cin nasara ba. Ba kullum mai hikima ne da abinci ba, ba kullum mai basira ne yake da wadata ba, ba kullum gwani ne yake samun tagomashi ba. Amma sa'a, da tsautsayi, sukan sami kowannensu.


Waɗannan su ne manyan jarumawan sojoji. Asahel ɗan'uwan Yowab Elhanan ɗan Dodo daga Baitalami Shamma daga Harod Helez daga Felet Aira ɗan Ikkesha daga Tekowa Abiyezer daga Anatot Sibbekai daga Husha Ilai daga Aho Maharai daga Netofa Heled ɗan Ba'ana daga Netofa Ittayi ɗan Ribai daga Gibeya ta Biliyaminu Benaiya na Firaton Hurai daga rafuffuka kusa da Ga'ash Abiyel daga Araba Azmawet daga Bahurim Eliyaba daga Shalim 'Ya'yan Yashen, maza, daga Gizon Jonatan ɗan Shimeya daga Harod Ahiyam ɗan Sharar daga Harod Elifelet ɗan Ahasbai Hefer daga Mekara Ahaija daga Felet Hezro daga Karmel Nayarai ɗan Ezbai Yowel ɗan'uwan Natan Mibhar ɗan Hagri Zelek daga Ammon Naharai daga Biyerot (Mai riƙe wa Yowab ɗan Zeruya makamai) Aira da Gareb daga Yattir Uriya Bahitte Zabad ɗan Alai Adina ɗan Shiza (Shi ne shugaba a kabilar Ra'ubainu, yana da ƙungiyarsa mai soja talatin tare da shi) Hanan ɗan Ma'aka Yoshafat daga Mitna Uzziya daga Ashtera Shama da Yehiyel 'ya'yan Hotam, maza, daga Arower Yediyel da Yoha 'ya'yan Shimri, maza, daga Tiz Eliyel daga Mahawa Yeribai, da Yoshawiya 'ya'yan Elna'am, maza Itma daga Mowab Eliyel, da Obida, da Yawasiyel daga Zoba.


“Saul da Jonatan ƙaunatattu ne, suna da bansha'awa, A raye suna tare, haka kuma a mace suna tare. Sun fi gaggafa sauri, Sun fi zaki ƙarfi.


Dawuda ya ce wa Ahimelek Bahitte, da Abishai, ɗan Zeruya, ɗan'uwan Yowab, “Wa zai tafi tare da ni zuwa sansanin Saul?” Abishai ya ce, “Zan tafi tare da kai.”


Sai ya tasar wa bin Abner haiƙan, bai kauce ba.


Ya mai da ƙafafuna kamar na barewa, Ya kiyaye ni a kan duwatsu.


Sauran jarumawan da suka zama talatin sun haɗu da waɗannan, Asahel, ɗan'uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo, daga Baitalami, Shamma da Elika, daga Harod, Helez, daga Felet, Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa, Abiyezer, daga Anatot, Sibbekai, daga Husha, Zalmon, daga Aho, Maharai, da Heled, ɗan Ba'ana, daga Netofa, Ittayi, ɗan Ribai, daga Gibeya ta Biliyaminu, Benaiya, daga Firaton, Hurai, daga kwaruruka kusa da Ga'ash, Abiyel, daga Araba, Azmawet, daga Bahurim, Eliyaba, daga Shalim, Yashen, daga Gimzo, Jonatan, ɗan Shamma, daga Harod, Ahiyam, ɗan Sharar, daga Harod, Elifelet, ɗan Ahasbai, daga Ma'aka, Eliyam, ɗan Ahitofel, daga Gilo, Hezro, daga Karmel, Nayarai, daga Arabiya, Igal, ɗan Natan, daga Zoba, Bani, daga Gad, Zelek, daga Ammon, Naharai, (mai ɗaukar wa Yowab, ɗan Zeruya makamai) daga Biyerot, Aira daga Gareb, daga Yattir, Uriya, Bahitte. Dukansu su talatin da bakwai ne shahararrun sojoji.


“Ka kuma san abin da Yowab ɗan Zeruya ya yi mini, yadda ya kashe shugabannin sojoji na Isra'ila su biyu, wato Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya zubar da jinin yaƙi a lokacin salama. Ya sa jinin yaƙi a kan ɗamararsa wadda take gindinsa, da kuma kan takalmansa da yake ƙafafunsa.


Da Yowab ɗan Zeruya, ya gane zuciyar sarki ta koma kan Absalom,


Ga yadda aka lasafta su bisa ga matsayinsu, da Ezer, da Obadiya, da Eliyab, da Mishmanna, da Irmiya, da Attai, da Eliyel, da Yohenan, da Elzabad, da Irmiya, da Makbannai.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ