2 Samaʼila 2:13 - Littafi Mai Tsarki13 Sai kuma Yowab, ɗan Zeruya, tare da fādawan Dawuda suka fita suka tafi tarye su a tafkin Gibeyon. Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe na tafkin. အခန်းကိုကြည့်ပါ။Sabon Rai Don Kowa 202013 Yowab wanda ake ce mamarsa Zeruhiya tare da waɗansu mutanen Dawuda suka fito suka haɗu da su tafkin Gibeyon, Suka zauna, waɗannan a wannan gefe, waɗancan a wancan gefe. အခန်းကိုကြည့်ပါ။ |
Sauran jarumawan da suka zama talatin sun haɗu da waɗannan, Asahel, ɗan'uwan Yowab, Elhanan, ɗan Dodo, daga Baitalami, Shamma da Elika, daga Harod, Helez, daga Felet, Aira, ɗan Ikkesha, daga Tekowa, Abiyezer, daga Anatot, Sibbekai, daga Husha, Zalmon, daga Aho, Maharai, da Heled, ɗan Ba'ana, daga Netofa, Ittayi, ɗan Ribai, daga Gibeya ta Biliyaminu, Benaiya, daga Firaton, Hurai, daga kwaruruka kusa da Ga'ash, Abiyel, daga Araba, Azmawet, daga Bahurim, Eliyaba, daga Shalim, Yashen, daga Gimzo, Jonatan, ɗan Shamma, daga Harod, Ahiyam, ɗan Sharar, daga Harod, Elifelet, ɗan Ahasbai, daga Ma'aka, Eliyam, ɗan Ahitofel, daga Gilo, Hezro, daga Karmel, Nayarai, daga Arabiya, Igal, ɗan Natan, daga Zoba, Bani, daga Gad, Zelek, daga Ammon, Naharai, (mai ɗaukar wa Yowab, ɗan Zeruya makamai) daga Biyerot, Aira daga Gareb, daga Yattir, Uriya, Bahitte. Dukansu su talatin da bakwai ne shahararrun sojoji.